Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Dr. Abdullah Al-Nafisi, farfesa a fannin kimiyyar siyasa a Jami'ar Kuwait, ya yi nuni da matsin lamba kai tsaye daga Washington a cikin wani rahoto game da tsoma bakin Amurka a harkokin ilimi na ƙasashen Larabawa na Tekun Farisa.
A cewar Al-Nafisi, Liz Cheney, 'yar tsohon mataimakin shugaban ƙasar Amurka Dick Cheney, a lokacin da ta kai ziyara Kuwait, ta yi kira da a cire wasu ayoyi daga Alƙur'ani Mai Tsarki da suke magana akan Yahudawa daga cikin manhajar ilimin makarantun ƙasar, sannan ta jaddada cewa ya kamata a gyara manhajojin karatun bisa ƙa'idodin da Amurka ke so.
Waɗannan kalamai suna nuna suka ga tsoma bakin siyasa da al'adu na Amurka a cikin tsarin ilimi da asalin ƙasashen yankin.
Menene haɗin kasashen larabawa da tsarin Amurka ko wace kasa da tsarin ta akwai dokar da ta ke bi.
Your Comment